Ana sa ran Birtaniya za ta fice daga tsibiran Malvinas bayan daidaita ikon mallakar tsibiran Chagos
2023-01-03 20:08:46 CMG Hausa
A ranar farko ta sabuwar shekarar 2023, mazauna tsibiran Chagos da ke tsakiyar tekun Indiya, sun yi maraba da wani labari mai dadi, bayan da firaministan Mauritius Pravind Jugnauth ya sanar da cewa, ya fara tattaunawa da Burtaniya kan batun ikon mallakar tsibiran Chagos da ake takaddama a kai. Wannan na nufin cewa, a hukumance an fara aiwatar da shirin mayar da tsibiran Chagos hannun Mauritius. Abin da kasashen duniya ke sa ran gani shi ne, bangaren Birtaniyya zai fuskanci batun tsibiran Malvinas tare da hanzarta dawo da yin tattaunawa da Argentina, bayan warware batun mallakar tsibiran Chagos.
Dangane da batun tsibiran Malvinas, kudurorin MDD da abin ya shafa sun yi bayani karara, kuma babu wani dalilin da zai sanya Birtaniyya ba za ta fice ba. Mulkin mallaka a karni na 21, ba zai samu wurin zama ba. (Ibrahim)