logo

HAUSA

Abdullahi Ayuba Konkiyel: Matakan yaki da cutar COVID-19 da China take dauka sun dace

2023-01-03 15:01:36 CMG Hausa

Abdullahi Ayuba Konkiyel, dan asalin jihar Bauchi ne, wanda ya taba nazartar ilimin harhada magunguna a wata jami’a dake birnin Nanjing na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin. A halin yanzu, yana ci gaba da zurfafa karatu a fannin kimiyyar bincike da gano cututtuka masu yaduwa a wata jami’a dake kasar Malaysia.

A hirar da ya yi da Murtala Zhang, malam Abdullahi Ayuba ya bayyana abubuwan da suka burge shi game da kasar Sin, inda ya yi fashin baki kan matakan da gwamnatin kasar take aiwatarwa, a fannin dakile cutar numfashi ta COVID-19, a cewarsa, matakan sun dace, kuma za su taka rawar a-zo-a-gani a fannin hana yaduwar cutar gami da raya tattalin arziki. (Murtala Zhang)