Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Lula murnar kama aiki a matsayin shugaban Brazil
2023-01-03 09:42:40 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murnar rantsar da shugaba Luiz Inacio Lula da Silva na Brazil. Cikin sakon na shugaba Xi, ya ce Sin da Brazil muhimman kasashe ne masu tasowa, wadanda ke da tasiri da saurin ci gaban tattalin arziki.
Shugaba Xi ya kara da cewa, tun kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen 2 yau shekaru 48 da suka gabata, akalarsu ta ci gaba da zurfafa, sakamakon kwazon da suke yi tare, inda suka samu bunkasuwa yadda ya kamata.
Kaza lika shugaban na Sin, ya ce yana dora muhimmancin gaske ga ci gaban hadin gwiwar Sin da Brazil bisa manyan tsare-tsare, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Lula, wajen taimakawa juna ta fuskar aiwatar da matakan ci gaba, gwargwadon yanayin da kasashe ke ciki, tare da martaba muhimman moriyar kasashen su, da habaka hadin gwiwasu a bayyane, da karfafa tsare-tsaren cudanya, da jagoranta, da ingiza kawancensu zuwa matsayi na gaba, na muhimmiyar dangantaka, da manufofi masu dogon zango, ta yadda hakan zai amfani kasashen biyu da kuma jama’ar su. (Saminu Alhassan)