An rantsar da sabon shugaban kasar Brazil
2023-01-03 16:44:15 CMG Hausa
Ga yadda aka rantsar da Luiz Inacio Lula da Silva a matsayin sabon shugaban kasar Brazil a birnin Brasilia, babban birnin kasar. A jawabin da ya gabatar, ya jaddada cewa, sabuwar gwamnatin sa za ta dukufa kan daidaita matsaloli da kalubalolin da kasar ke fuskanta, don dawo da kasar cikin jerin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya. (Lubabatu)