logo

HAUSA

“Ziri daya da hanya daya” da ke haifar da alfanu ga al’ummar duniya

2023-01-03 22:01:38 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, aka kammala kashi na farko na layin dogo mai amfani da lantarki a jihar Lagos, tarayyar Nijeriya, wanda ke zama irinta ta farko a yammacin Afirka, haka kuma karin nasara da aka cimma a kokarin aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, ko kuma “Belt and Road Initiative” a Turance. Da yake kaddamar da aikin, gwamnan jihar Lagos Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya bayyana shi a matsayin wanda zai saukaka matsalar zirga-zirga da ake fuskanta a jihar, kana abin koyi ga Nijeriya da ma sauran kasashen yammacin Afirka wajen shimfida layukan dogo.

A cikin shekarar da ta gabata, an aiwatar da hadin gwiwar “ziri daya da hanya daya” tare da dimbin nasarori, inda a cikin watanni 11 na farkon shekarar, jimillar kudin ciniki a tsakanin kasar Sin da sauran abokananta da suka amshi shawarar ya karu da kaso 20.4% duk da kalubalolin da aka fuskanta a duniya, baya ga jerin shirye-shiryen da aka yi nasarar cimmawa, ciki har da kammala gine-ginen cibiyar kasuwanci a sabuwar fadar mulkin kasar Masar dake kusa da birnin Alkahira, da fara gwajin zirga-zirgar layin dogo na zamani na farko na kasashen kungiyar ASEAN, da fara aiki da gadar Peljesac a kasar Croatia da ma tashar samar da wutar lantarki ta Karot a kasar Pakistan da dai makamantansu. Ban da wannan, a shekarar, karin wasu kasashe biyar sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa tare da kasar Sin bisa shawarar ziri daya da hanya daya.

Bana ne ake cika shekaru 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya. A cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce, kasashen da suka amshi shawarar sai karuwa suke ta yi, wadanda suka yi ta inganta hadin gwiwarsu, kuma shawarar na ta kara samun karbuwa daga kasa da kasa. Shawarar da aka aiwatar ta samar da gadoji da tashoshin ruwa da hanyoyi marasa lisaftuwa a kasashen da suka karbi shawarar, wadanda suka kyautata rayuwar miliyoyin al’ummar kasashen, lamarin da ya shaida karfin hadin gwiwar kasa da kasa.

A wani sabon mafari, kasar Sin na sa ran aiwatar da shawarar tare da kasashen duniya cikin karin wasu shekaru 10 masu zuwa, ta yadda shawarar za ta haifar da karin alfanu ga kasashen duniya da al’ummominsu.(Lubabatu)