logo

HAUSA

'Yan sanda a Najeriya sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina

2023-01-03 11:52:27 CMG Hausa

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar, ta ce jami'anta sun yi nasarar harbe wani mahari guda, yayin dauki ba dadi da suka yi da gungun 'yan bindiga da suka yi yunkurin farwa wani shingen bincike.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin rundunar a jihar Katsina Gambo Isah, ya ce 'yan sanda dake aiki a shingen bincike kan titin Magamar-Jibia a karamar hukumar Jibia, sun yi musayar wuta da 'yan bindigar ne a jiya Litinin, inda daga karshe suka hallaka daya daga cikinsu, kana wasu da dama suka tsere da harbin bindiga.

Kana ya ce akwai 'yan sanda 2 da su ma suka jikkata yayin fafatawar. Kakakin ya ce suna ci gaba da farautar 'yan bindigar da suka tsere.  (Saminu Alhassan)