logo

HAUSA

A Najeriya gwamnatin kasar na ci gaba da rabon tallafi ga dubban mutanen da ambaliyar ruwan 2022 ya tagaiyara

2023-01-02 15:04:31 CMG Hausa

A ranar 1 ga wata ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar NEMA ta ci gaba da rabon kayayyakin tallafi ga daruruwan mutanen da suka gamu da annobar ambaliyar ruwa a jihar Kano dake arewacin kasar.

Kayayyakin da aka rabar sun kunshi kayan abinci da na gini.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da wannan rahoto.