logo

HAUSA

RCEP ta zama abin koyi ga hadin gwiwar tattalin arzikin shiyya shiyya

2023-01-02 15:33:28 CMG Hausa

Jiya Lahadi 1 ga wata, ake cika shekara daya da yarjejeniyar huldar abokantaka ta hadin gwiwar tattalin arzikin shiyya shiyya daga dukkan fannoni wato RCEP ta fara aiki a hukumance, yarjejeniyar RCEP da ta samar da damammakin cinikayya ga kamfanoni da dama.

A tashar teku ta birnin Tianjin, wani ma’aikacin kamfanin samar da kayayyakin dake shafar man fetur ya bayyana cewa, “Kayayyakinmu suna kara samun karbuwa a kasar Japan!”. An ga kayayyakin kamfanin sun tashi daga birnin Inchon na kasar Koriya ta kudu domin zuwa birnin Tianjin na kasar Sin, daga baya an yi jigilar su zuwa kasar Japan ba tare da biyan harajin kwastam ba, wannan wata dama ce ta habaka cinikayya da kamfanonin da abin ya shafa suka samu tun bayan da aka fara aiwatar da yarjejeniyar RCEP.

Kungiyar ASEAN ce ta ba da shawarar daddale yarjejeniyar RCEP, wadda ta kunshi kasashe mambobin kungiyar guda goma da kasar Sin da Japan da Koriya ta kudu da kuma New Zealand. RCEP, yarjejeniyar cinikayya maras shinge ce da ta shafi al’ummar kasashe da tattalin arziki da cinikayya mafiya yawa. A cikin shekarar 2022, wato bayan da ta fara aiki a farkon shekarar, kasashe 13 daga cikin 15 ne suka daddale yarjejeniyar. A halin yanzu, tattalin arzikin duniya yana fama da matsala, don haka ana daukar yarjejeniyar a matsayin wani “haske” wanda zai taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ta shiga yarjejeniyar, lamarin da ya nuna aniyyarta ta kara bude kofa ga ketare.

A nata bangaren, shigar kasar Sin cikin yarjejeniyar tana da muhimmanci matuka, saboda tattalin arzikin kasar Sin ya kai kaso kusan 60 bisa dari da daukacin yarjejeniyar, kuma kasar Sin tana samar da sabbin damammaki ga duk duniya bisa sabon ci gabanta. (Jamila)