logo

HAUSA

Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin Ta Gudanar Da Taron Kwamitinta

2022-02-27 20:26:41 CRI

Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC karo na 13, wadda ta kasance majalisar koli ta kasar, ta fara gudanar da taronta karo na 33 a yau Lahadi, domin share fagen taron shekara-shekara na NPC karo na 13 dake tafe, wanda za a bude a ranar 5 ga watan Maris.

‘Yan majalisar sun kammala aikin duba rahoton zaunannen kwamitin na NPC. Kuma za a gabatar da rahoton a gaban taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin a watan Maris, domin yin mahawara kansa.

Taron ya yi nazari kan daftarin doka game da batun mukaman sojojin rundunar ‘yantar da al’umma ta PLA dake bakin aiki, da daftarin doka dake shafar kafa kotun kula da al’amurran kudi ta Chengdu-Chongqing, da kuma rahoton da ya shafi aiwatar da dokar da kwamitin NPC ya zartar game da batun matakan sauraron shara’ar da ta shafi kararraki game da hakkin mallakar fasahar kira.(Ahmad)

Ahmad