logo

HAUSA

Burikan wakilai mata na NPC daga jihar Xinjiang

2021-03-08 14:41:35 CRI

Yanzu ana taron shekara shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta NPC a nan birnin Beijing, wadda ta kasance hukumar koli ta kasar Sin ta fuskar kafa doka. Inda a madadin al’ummomin kasar Sin na kabilu daban daban da sassa daban daban, wakilan jama’ar kasar Sin kimanin 3000 da aka zabe su daga wurare daban daban ke tattauna da zartas da rahoton aiki na gwamnatin kasar Sin da dai sauran muhimman rahotannin da ke da nasaba da tafiyar da harkokin kasar. A cikin wadannan wakilan, yawan mata ya kai kaso 24.9. To a cikin shirinmu na yau, zan gabatar muku da labaran wasu daga cikinsu kan yadda suke ba da shawarwarinsu don ci gaban kasar a matsayinsu na wakilan jama’ar Sin.

Burikan wakilai mata na NPC daga jihar Xinjiang_fororder_微信图片_20210308141142

Cui Jiuxiu mai shekaru 27 da haihuwa, wata wakiliya ce daga jihar Xinjiang. Tana aiki a filin samar da ire-iren kayayyakin lambu masu nagarta na gundumar Shufu a yankin Kashgar da ke kudancin jihar Xinjiang, a matsayin shugaban filin. Bayan da Cui Jiuxiu ta gama karatu daga jami’a a shekarar 2014, ta bar garinta da ke gabashin kasar Sin, kuma ta je jihar Xinjiang da ke yammacin kasar, bisa kiran gwamnatin kasar Sin na “zuwan yammacin kasar don ba da gudummawa ga ci gaban wurin”.

Yayin da take tabo magana kan gundumar Shufu da take yanzu, Cui Jiuxiu ta gaya min cewa, yanzu gundumar ta riga ta zama garinta na biyu, ganin yadda take aiki take zama a nan har na tsawon shekaru 7. A cikin wadannan shekarun da suka gabata, Cui Jiuxiu ta ganam ma idanunta kan yadda gundumar, yankin Kashgar, har ma duk jihar Xinjiang suka fita daga kangin talauci. Cui Jiuxiu ta ce

“A da, mazauna wurinmu kan ce, idan wani ya ci fanke mai fadi wato Nang daya a rana guda, to, ya ji dadin zamansa. Idan wani ya ci Nang guda hudu a rana guda, wallahi tabbas wannan ne lokacin murnar sallah. Amma yanza ba za a ci gaba da tantance dadin zaman rayuwar wani bisa yawan Nang da ya yi, sabo da ana iya cin komen da yake so. Gaskiya zaman mazauna wurinmu ya samu kyautatuwa sosai har ma ya wuce abin da suka zata.”

Ba za a kara jin dadin zaman rayuwa ba, sai dai bayan da ya sha wahala, a cewar Cui Jiuxiu, kuma wannan ya zama dalilin da ya sa ta gabatar da wasu shawarwari a yayin wannan taron NPC, wadanda ke da nasaba da ci gaba da aikin farfado da yankunan karkara, a kokarin kara kyautata zaman rayuwar mazauna jihar Xinjiang. Alal misali, tana fatan gundumomin yankin Kashgar zai samu damar kara farfadowa ta hanyar raya sana’o’in da ke da yanayin musamman bisa manufofin gwamnatin Sin kamar kafa cibiyar samar da fanken Nang mafi girma ta duk fadin kasar Sin a yankin Kashgar. Cui ta kara da cewa,

“Da ba a sha wahala ba, da ba a san dadi ba. Yanzu mazauna wurin Kashgar na jin dadin zamansu sosai. Don haka a matsayina na wata wakiliyarsu, ina fatan bisa kokarina na gabatar da shawarar mai dacewa, za a iya ci gaba da kiyaye sakamakon yaki da fatara, da ma kara bunkasar yankunan karkara, ta yadda mazauna wurinmu za su iya cimma burinmu na neman samun zama mai wadata.”

Burikan wakilai mata na NPC daga jihar Xinjiang_fororder_微信图片_20210308141254

Urnisa Carder ‘yar kabilar Ugyur ita ma wata wakiliya ce daga jihar Xinjiang. Madam Urnisa ita ce mataimakiyar shugaban cibiyar yayata fasahohin shuka bishiyoyin ‘ya’yan itatuwa na birnin Turpan da ke jihar Xinjiang. Bayan da ta gama karatu daga jami’a, Urnisa ta koma garinta, sa’an nan ta kaddamar da aikinta na nazarin fasahohin zamani na shuka bishiyoyin inabi. Domin kara yawan kudin shiga da mazauna wurin ke samu daga fannin shuka bishiyoyin inabi, ta ziyarci dukkan kauyukan da ke shukar bishiyoyin inabi domin koyar da fasahohin shukawa, a kokarin magance matsaloin da manoma ka iya gamuwa da su. Bisa kokarin da ta yi har na tsawon shekaru fiye da 20, yanzu inabi na yankin Turpan na da suna sosai har ma ya zama alama ta wurin. Manoma masu shukka inabi kuwa sun samu wadata. An ce, ya zuwa kashen shekarar 2019, yawan fadin shuka bishiyoyin inabi a yankin Turpan ya kai hekta dubu 38, inda aka samar da inabi tan miliyan 1.22, kaso 46 na yawan kudin shiga ga manoma wurin kuwa daga aikin da ke da nasaba da inabi.

A matsayin wata mai rike da fasahar noma, abin da ya fi burge Urnisa a cikin rahoton aikin gwamnati da firaminista Li Keqiang ya gabatar a yayin taron shekara shekara na NPC na bana shi ne yadda kasar Sin za ta mai da hankali kan kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, musamman ma a fannin ayyukan gona. A ganinta, kimiyya da fasaha karfi ne mafi muhimmanci ga ci gaban kasa. Urnisa ta ce,

“Kasar Sin wata babbar kasa ce mai yawan al’umma fiye da biliyan 1.3, kuma wata babbar kasa ce ta ayyukan gona. Ba za mu iya samun abin dogoro da kai ba sai dai a raya sha’anin nomanmu ta hanyar raya fasahohin zamani. Idan mun samu isassun hatsin da ke iya biyan bukatun al’ummarmu, to za mu iya ji dadin zamanmu.”

Urnisa ta kuma bayyana cewa, Turpan wani muhimmin zango ne a kan hanyar siliki tun can can da, wanda ya hada da al’adun gabashi da yammacin duniya sosai. Bayan da aka raya shi a wadannan shekarun da suka gabata, yanzu jirgin kasa, jirgin sama da dai sauran muhimman ababen more rayuwa sun samu bunkasa sosai a nan. Bisa wannan yanayi mai kyau da Turpan ke da shi, Urnisa ta gabatar da wata shawara a yayin taron NPC na bana, wato kafa wata cibiyar rarraba busassun ‘ya’yan itatuwa mafi girma ta kasar Sin a Turpan. Tana mai cewa,

“Idan wannan cibiyar rarraba busassun ‘ya’yan itatuwa ta kafu, to za ta taimaka sosai wajen samar da guraban ayyukan yi ga mazauna wurinmu, musamman ma ga manomanmu da ke Turpan, lamarin kuwa da zai ba da taimako ga aikin farfado da yankunan karkara na kasarmu.”

Hakika dai, Ban da Cui Jiuxiu da Urnisa Carder, ko wane wakilin jama’ar kasar Sin na sauke nauyin da ke wuyansu wajen yin bincike da ma rubuta shawarwari domin gabatar da su ga taron NPC, a kokarin ba da taimako yayin da ake tsara manufofin kasar, ta hakan wakilan sun bayar da gudummawarsu ga ci gaban kasar.

Kande