logo

HAUSA

Kasar Sin na maraba da ‘yan sama jannati na kasashen waje

2021-10-15 10:51:21 CMG

Kasar Sin na maraba da ‘yan sama jannati na kasashen waje_fororder_211015-astronaut-Faeza

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin, ta ce tana maraba da ‘yan sama jannati daga kasashen ketare sun shiga cibiyarta dake sararin sama.

Daraktan hukumar Lin Xiqiang ya bayyana yayin wani taron manema labarai gabanin harba kumbon Shenzhou-13 da aka shirya yi a gobe, da misalin karfe 12:23 na rana agogon Beijing daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan cewa, kasar Sin na maraba da ‘yan sama jannati zuwa cibiyarta dake sararin samaniya domin gudanar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa.

Ya ce ana hadin gwiwa a fannin zabe da horar da ‘yan sama jannati tsakanin Sin da kasashen ketare.

Haka kuma, wasu ‘yan sama jannati na kasar Sin sun karbi horo a Rasha. Yana mai cewa, Ye Guangfu ya kammala karbar horon da hukumar kula da sararin samaniya ta Turai ESA ta shirya a 2016.

Ya kara da cewa, hadin gwiwa a fannin sararin samaniya tsakanin kasa da kasa na da matukar muhimmanci wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya ga daukacin bil adama.

Kasar Sin tana hada hannu da kasashe kamar Rasha da Jamus da Faransa da Italiya da Pakistan, da wasu hukumomi kamar ofishin MDD mai kula da harkokin da suka shafi sararin samaniya da hukumar ESA ta Turai. (Fa’iza Mustapha)

Faeza