logo

HAUSA

Samuel Iqpefan: Yan wasan Afirka za su iya shiga gasannin Olympics na lokacin hunturu idan sun samu karin tallafi

2022-02-24 15:52:29 CRI

Samuel Iqpefan: ‘Yan wasan Afirka za su iya shiga gasannin Olympics na lokacin hunturu idan sun samu karin tallafi_fororder_626

Dan wasan hunturu daya tilo daga tarayyar Najeriya, da ya halarci gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing Samuel Iqpefan, ya ce kyakkyawan shiri da kasar Sin ta yi wajen shirya gasa mai inganci ne, ya sanya Najeriya ta shiga gasar. Samuel Iqpefan ya ce, duk da shi kadai ne ya wakilci Najeriya a wasan zamiyar kankara ta skiing, shi da sauran ‘yan uwansa masu wasannin motsa jiki na lokacin hunturu, za su iya ci gaba da shiga gasannin kasa da kasa, idan har an kara samar musu da tallafin da ya kamata.

An haife Samuel Iqpefan a kasar Faransa, ya kuma fara koyon wasan zamiya na skiing tun yana da shekaru 6 a duniya. Daga bisani ya gano cewa, a Najeriya ma akwai kungiyar horas da wasan na ski, hakan ya ba shi sha’awa ya kuma burge shi. A matsayin sa na matashi, wanda daya daga mahaifansa dan Najeriya ne, ya zabi zama dan Najeriya a shekarar 2019, ya kuma wakilci kasar a gasannin kasa da kasa a wasan ski.

A karshen gasar Olympics ta birnin Beijing da aka kammala kwanan nan, Samuel Ikpefan ya karbi gayyatar tattaunawa daga kafar watsa labarai ta kasar Sin. Kuma a matsayin sa na dan Najeriya mai wasan ski, ya yi farin ciki da hakan. Abun alfahari ne kwarai, wanda ya nunawa duniya cewa, ‘yan wasan Afirka na iya yin wasan ski, su kuma yi nasarar shiga manyan gasanni.

Samuel ya ce mutane da dama ba sa ganin akwai wata alaka, tsakanin wasannin lokacin zafi da na lokacin hunturu, kuma wakiltar Najeriya a wasannin hunturu yana da muhimmanci, saboda hakan na nunawa duniya cewa, ‘yan wasa na iya shiga a dama da su, ko da sun fito daga kasashen da ba kasafai ake yin wasannin lokacin hunturu ba. Hakan zai share fagen baiwa karin mutane damar shiga wasannin a gaba. Kaza lika wannan mataki zai ingiza karin mutane su shiga wasannin na hunturu.

Dan wasan ya ce "Shiga wasannin hunturu na Olympics a birnin Beijing da na yi, zai sharewa karin ‘yan wasa daga Afirka dake sha’awar irin wadannan wasanni fage, kuma zan ci gaba da yin hakan a nan gaba”.

Samuel wanda a yanzu ke da shekaru 30 da haihuwa, ya shiga gasar Olympics ta lokacin hunturu a karon farko, inda ya zamo na 73, a wasan zamiya mai dogon zango, ko da yake bai kammala gasar da ya shiga da kilomita 15 ba.

Ga ‘yan wasan motsa jiki na Afirka, abu ne mai wahala su cimma burin su na shiga wasannin hunturu na Olympics. Samuel ya ce yana bukatar taimako domin samun horo mai inganci, da kayan wasa masu nagarta. Sabo da haka ne ma, Samuel ya kashe dukkanin kudaden sa domin cimma wannan buri, ta yadda ya zame masa wajibi ya roki tallafin al’umma domin samun kudaden rajista, da na sufuri, da na kayan wasa da sauran su, kafin ya samu damar halartar gasar ta Olympics.

Kasancewar ya san wadannan wahalhalu, Samuel yana da burin ganin mahukuntan kasashen Afirka sun waiwayi fannin wasannin hunturu, su baiwa harkar muhimmanci, tare da tallafawa wasannin. Matashin ya ce yana fatan ma’aikatar wasanni ta Najeriya, za ta ware wani kasafi domin ba shi damar wakiltar kasar a wasannin kankara na duniya, da na FIS, da wanda sauran hukumomin kasa da kasa ke shiryawa.

Samuel ya ce duk da cewa ‘yan wasan hunturu na nahiyar Afirka, ba su da cikakkiyar kwarewa, amma suna da karsashi na shiga a dama da su, don haka ya karfafa gwiwar matasan Afirka dake son shiga wasannin hunturu, yana mai cewa: "Ba bukatar karaya, a nan gaba, matasa ‘yan wasa daga Najeriya za su kara shiga a dama da su. Za su halarci karin wasannin hunturu, kuma mutane da yawa za su samu zarafin wakiltar Najeriya a gasannin lokacin hunturu.