logo

HAUSA

Motsa jiki yana amfanawa matan da nauyinsu ya wuce misali wajen daidaita matsalolin al’adarsu

2022-02-23 07:58:11 CRI

Motsa jiki yana amfanawa matan da nauyinsu ya wuce misali wajen daidaita matsalolin al’adarsu_fororder_src=http___pic2.zhimg.com_v2-1ae38435cf3bb87137cf87e46f52ff61_1200x500&refer=http___pic2.zhimg(1)

Wani nazarin da ke karkashin shugabancin jami’ar Queensland ta kasar Australiya ya shaida mana cewa, motsa jiki yana taimaka wa matan da nauyinsu ya wuce misali wajen daidaita matsalolin al’adarsu, kamar zubar jini da yawa da saba lokacin da ya kamata al’ada ta rika zuwa a ko wane wata.

Masu nazarin sun tantance bayanan da suka shafi mata dubu 10 da 618, wadanda aka tattara cikin shekaru 15 don gudanar da nazari kan lafiyar mata ‘yan kasar Australiya. Sun yi nazari kan alakar da ke tsakanin wasannin motsa jiki, da mizanin jikin mata, wadanda suka hada da zubar jini da yawa a lokacin da al’ada ta zo, da saba lokacin da ya kamata al’ada ta rika zuwa a ko wane wata da dai sauran su.

Masu nazarin daga kwajejin nazarin motsa jikin dan Adam da kimiyyar abubuwa masu gina jiki na jami’ar Queensland ta kasar Australiya sun gano cewa, matan da nauyinsu ya wuce misali sun fi saukin gamuwa da matsalolin al’ada, alal misali, zubar jini da yawa a lokacin da al’ada ta zo, da saba lokacin da ya kamata al’ada ta rika zuwa a ko wane wata, idan an kwatanta su da takwarorinsu wadanda suke da daidaiton nauyin jiki ko kuma sirira. Amma sakamakon kara motsa jiki, barazanar zubar jini da yawa a lokacin da al’ada ta zo da suke fuskanta ta ragu da kaso 19 cikin dari.

Masu nazarin sun ci gaba da cewa, a baya a kan gudanar da makamancin nazarin kan ‘yan wasa mata, amma nazarinsu ya gudana ne kan matan da ba sa aikin wasannin motsa jiki, lamarin da ya jaddada muhimmancin lafiyar jiki kan karewa da kuma daidaita matsalolin al’ada.

Dangane da yadda ake motsa jiki a zaman yau da kullum, madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta ba mu shawarar cewa, ya fi kyau mata su rika tafiya da kafa, yin iyo, hawan keke da dai sauransu a kullum, wadanda suke taimakawa wajen daidaita matsalolin al’ada, kana kuma suna kare matan da nauyinsu ya wuce misali daga wasu cututtukan da su kan kamu da su, alal misali, ciwon hawan jini, ciwon sukari da ciwon zuciya.(Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan