logo

HAUSA

Matasa fiye da kaso 80 a duniya ba sa motsa jiki yadda ya kamata

2021-04-19 11:53:24 CRI

Matasa fiye da kaso 80 a duniya ba sa motsa jiki yadda ya kamata_fororder_u=1082915812,2888921276&fm=26&fmt=auto&gp=0

Kwanan baya, hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta ba da wata sanarwa, inda ta ce, wani sabon nazari da aka gudanar karkashin shugabancinta ya nuna cewa, matasa fiye da kaso 80 a duniya ba su motsa jiki isasshe, musamman ma ‘yan mata, lamarin da zai illanta lafiyarsu. Hukumar WHO ta yi kira ga gwamnatoci da su gaggauta daukar matakai, a kokarin ganin suna kara motsa jiki.

Masu nazari sun bibibi matasa miliyan 1 da dubu 600 wadanda shekarunsu suka wuce 11 amma ba su kai 18 a duniya ba a kasashe da yankuna 146 a duniya daga shekarar 2001 zuwa 2016. Inda suka gano cewa, a shekarar 2016, ‘yan makaranta da yawansu ya kai kaso 81 a duniya ba sa bin shawarar WHO, wato ba sa motsa jiki sosai a kalla na awa daya a ko wace rana, ciki had da kaso 78 na maza da kuma kaso 85 na mata.

Mene ne illar karancin motsa jiki? Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan dake Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, karancin motsa jiki yana illanta lafiyar matasa. Idan sun motsa jiki sosai, to, za su ci gajiya sosai a tunani da jiki. A kan ba da shawarar gaggauta daukar matakai don matasa su kara motsa jiki.

Masu nazarin sun kalubalanci gwamnatoci da su gaggauta fito da manufa ko kyautata manufa, su yi amfani da albarkatu masu ruwa da tsaki, su kuma taimakawa matasa kara motsa jiki, alal misali, samar da yanayi mai tsaro don matasa su je karatu da kafa ko hawan keke.

Har ila yau, sakamakon nazarin ya shaida cewa, daga shekarar 2001 zuwa 2016, yawan matasa maza wadanda ba sa motsa jiki isasshe ya ragu zuwa kaso 78 daga kaso 80, yayin da yawan matasa mata wadanda ba sa motsa jiki isasshe ya kai kaso 85, wadannan alkaluma ba su sauya ba. Matasa ‘Yan mata ba su motsa jiki kamar yadda matasa maza suke yi. Kamata ya yi a kara samar wa ‘yan mata zarafi don biyan bukatunsu da abin da suke sha’awa, ta haka za su kara motsa jiki.

A yayin babban taron lafiyar kasa da kasa na shekarar 2018, kasashen duniya sun tsara wata manufa, don rage yawan matasan da ba sa yin isasshen motsa jiki zuwa kaso 70 a shekarar 2030. Ya zuwa yanzu matasa ba sa yin isasshen motsa jiki a duniya baki daya.  (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan