logo

HAUSA

Masana Sun Isa Hong Kong

2022-02-18 14:11:11 CRI

Tawagar masana masu ilmin cututtuka masu yaduwa ta babban yankin kasar Sin, ta isa Hong Kong da yammacin ranar 17 ga watan nan, don taimakawa yankin wajen yaki da annobar cutar COVID-19, daga fannonin binciken asalin cutar, da nazarin yaduwar annobar, da ma barazanar yaduwarta, a kokarin taimakawa Hong Kong dakile yaduwar annobar cikin hanzari.

Kwanan baya, an sha fama da annobar ta COVID-19 a Hong Kong. Don haka gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta kafa rukunin musamman don mara wa Hong Kong baya, wajen yaki da annobar. Kuma bisa bukatun mahukuntan Hong Kong, ta dauki matakai nan da nan.

Ban da wannan tawagar da aka tura, za kuma a bukaci sassa daban daban na kasar su taimakawa mahukuntan Hong Kong, wajen dakile yaduwar annobar cikin sauri. (Tasallah Yuan)