logo

HAUSA

Ci Gaban Demokuradiyyar HK Karkashin Manufar “Kasa Daya Amma Tsarin Mulki Biyu”

2021-12-20 19:58:06 CRI

An kammala zaben ‘yan majalisar kafa doka karo na 7, na yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Yau Litinin, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fidda takardar bayani mai taken "Ci gaban demokuradiyyar Hong Kong karkashin manufar ‘kasa daya amma tsarin mulki biyu’", inda aka yi karin bayani kan tarihin demokuradiyyar Hong Kong, tare da bayyana matsayin gwamnatin tsakiyar kasar Sin kan goyon bayan Hong Kong, da raya tsarin demokuradiyya bisa hakikanin halin da take ciki.

A can da kasar Birtaniya ta dauki shekaru 150 tana mulkin mallaka a Hong Kong, kuma sau da dama ta hana yin gyare-gyare kan harkokin demokuradiyya a yankin, don haka babu demokuradiyya a Hong Kong. Amma bayan da Hong Kong ta koma hannun kasar Sin a shekarar 1997, a karo na farko mazauna yankin sun samu damar tafiyar da harkokinsu da kansu, karkashin manufar “kasa daya amma tsarin mulki biyu”.

Abubuwan da suka faru cikin shekaru 24 da suka wuce sun nuna cewa, neman samun demokuradiyya mai salon kasashen yammacin duniya ba bisa sanin ya kamata ba, ya jefa Hong Kong cikin rudani ne kawai. Wajibi ne Hong Kong ta bi hanyarta a fannin raya demokuradiyya. Ya zama dole da ta bi manufar “kasa daya amma tsarin mulki biyu” da manyan dokokin yankin, kana a bari ‘yan kishin kasa su gudanar da harkokin yankin na Hong Kong bisa hakikanin halin da ake ciki a yankin, kuma bisa doka da tsari.

Har kullum gwamnatin tsakiyar kasar Sin, na ba da jagora kan bunkasuwar demorakudiyyar Hong Kong, da nuna goyon baya da kuma kara azama a kai. Tana kuma kiyaye manyan muradun mazauna Hong Kong baki daya. Duk yunkurin da ake yi na barnata demokuradiyyar Hong Kong zai ci tura. A yanzu haka dai demokuradiyyar Hong Kong tana fuskantar kyakkyawar makoma. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan