logo

HAUSA

An Kammala Gwajin Karshe Na Liyafar Bikin Bazara Na CMG Na Shekarar 2022

2022-01-30 16:35:16 CRI

An Kammala Gwajin Karshe Na Liyafar Bikin Bazara Na CMG Na Shekarar 2022_fororder_cmg

A ranar Asabar an gudanar da gwaji na biyar na gagarumar liyafar bikin bazara na shekarar 2022 na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG. Dukkan shirye-shirye da ayyukan gwaji na hadin gwiwa na liyafar bikin bazarar na wannan shekara sun kammala, kuma an riga an kammala dukkan shirye-shiryen watsa shiri na kai tsaye na liyafar bikin bazara ta bana.

A jajibirin bikin bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, CMG zai gabatar da wata liyafa mai cike da al’adun kasar Sin kuma mai kayatarwa ga masu kallo daga dukkan sassan duniya. Babban taken gagarumar liyafar bikin bazarar ta wannan shekara ya hada da, tunawa da cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, bunkasa cigaban yankunan karkara, kiyaye muhallin halittu, gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu, da kuma nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin binciken sararin samaniya.

Za a nuna manyan fasahohi daban daban a liyafar bikin bazara ta wannan shekara. A karon farko, an samar da fasahar amfani da allon nuna bidiyo na LED na 720-degree, tare da fasahohin AR, da XR da sauran fasahohin zamani. Akwai kuma fasahar 8K wanda za ta baiwa masu kallo wata sabuwar hanyar kallon liyafar.

Za a watsa kasaitacciyar liyafar bikin bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ne da misalin karfe 8 na dare a ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2022, agogon Beijing.(Ahmad)

Ahmad