CMG na kokarin gabatarwa kasashen Afirka liyafar bikin bazarar Sin
2022-02-02 16:15:25 CRI
A ranar 31 ga watan Janairu, an gudanar da bikin “Kallon liyafar bikin bazara, da Maraba da gasar Olympics ta lokacin hunturu” a cibiyar “Two Rivers” dake birnin Nairobi na kasar Kenya.
Wannan shi ne karo na farko da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya gabatar da liyafar bikin bazara kai tsaye da fasahar 4K a kasar waje. Haka kuma, an kunna fitilu masu launin ja, a babbar taya mai juyawa, wadda ta kasance mafi girma a nahiyar Afirka, domin kara bayyanawa al’ummomin nahiyar Afirka ma’anar liyafar bikin bazarar kasar Sin, da ma al’adun kasar Sin.
Haka kuma, an kunna fitilu masu nuna alamar CMG, da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, a cibiyar cinikin kasa da kasa ta Nairobi, wato gini mafi tsayi a gabashin nahiyar Afirka.
An cimma nasarar gabatar wa al’ummomin nahiyar Afirka, liyafar bikin bazarar kasar Sin, da ma al’adun kasar Sin, ta hanyar gudanar da wannan biki. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)