logo

HAUSA

Putin ya yi hira da shugaban CMG

2022-02-03 15:39:19 CRI

Putin ya yi hira da shugaban CMG_fororder_ea2e-2780e4e95bbde2a2e0f21aebed3e3de2

A gabanin bude gasar Olympic ta lokacin sanyi dake tafe a birnin Beijing, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya zanta da shugaban babban rukunin gidan rediyo da telibiji na kasar Sin CMG Shen Haixiong ta rubutaccen jawabi.

Shugaba Putin ya nuna cewa, Rasha tana tsayin daka kan yayata ruhin Olympic tare da nuna adawa da siyasantar da gasar, da amfani da gasar wajen matsa lamba kan sauran kasashe da yin takara maras adalci da nuna bambancin ra’ayi.

Ya ce, kasar Sin sahihiyar abokiyar Rasha ce a dandalin duniya. Kuma kasashen biyu na da ra’ayi daya kan yawancin batutuwa dake shafar duniya. Ban da wannan kuma, suna hada kai da sulhutawa sosai bisa tsarin MDD da BRICS da SCO da G20 da APEC da EAS da sauransu. Matakin da ya taka rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a duniya baki daya.

Rahotanni na cewa, shugaba Putin zai halarci bikin bude gasar Olympic ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 dake tafe a birnin Beijing. (Amina Xu)