logo

HAUSA

CMG zai nuna kasaitaccen shirin talibijin na murnar bikin bazara a jajibirin sabuwar shekara

2022-01-15 19:12:30 CRI

CMG zai nuna kasaitaccen shirin talibijin na murnar bikin bazara a jajibirin sabuwar shekara_fororder_gala CMG

Guinness World Records ya amince da kasaitaccen shirin talibijin na murnar bikin bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin da babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG yake shiryawa a kowace shekara, a matsayin shirin talabijin da aka fi kallo a duniya.

A tsawon shekaru 40, jama’a na kallon kasaitaccen shirin talibijin na murnar bikin bazara a jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, a matsayin wani muhimmin bikin murnar sabuwar shekara ga iyalan Sinawa a ko’ina a duniya. Bana shekara ce ta Damisa a bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, kuma kamar yadda aka saba, a bana ma za a gabatar da shirye-shirye masu kayatarwa, kamar su wake-wake da raye-raye, da wasannin barkwanci, da wasan kwaikwayon gargajiya na opera a shirin. Shirin mai cike farin ciki da annashuwa ya hade al'ada da zamani waje guda, jama’a na shakatawa cikin raha.

Ko ina kake, ka kasance kusa da akwatin talibijin dinka don kallon kasaitaccen shirin na bana. A ranar 31 ga Janairu, 2022, agogon Beijing, da karfe 8 na dare a jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, don mu kalli shirin tare!

Ibrahim Yaya