logo

HAUSA

Muhimman labarai 10 da suka faru a duniya a shekarar 2021 da CMG ya fitar

2021-12-29 09:12:23 CRI

Masu iya magana na cewa, "shekara kwana" a ranar Jumma’a 31 ga watan Disamba na shekara ta 2021 miladiya ta kawo karshe, kuma kamar sauran shekaru da suka gabaci wannan shekara, abubuwa da dama sun faru, kama daga na ban-al'ajabi, mamaki, tausayi, bajinta, takaici, tashin hankali da dai sauransu.

Muhimman labarai 10 da suka faru a duniya a shekarar 2021 da CMG ya fitar_fororder_211229世界21049-hoto1

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin(CMG) ya fitar da wasu muhimman labarai guda 10 da suka dauki hankalin duniya a shekarar 2021 dake shirin karewa. Kadan daga cikin wadannan muhimman labarai sun hada da na farko, shugaban kasar Sin Xi Jinpjng ya gabatar da shawarar daukar matakan raya kasa da kasa, da yaki da annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar sassan duniya, sakamakon kalubale na rashin daidaiton alluran riga kafin cutar, da yadda wasu kasashen yamma ke siyasantar da aikin gano asalin kwayar cutar. Da kuma cikar JKS shekaru 100 da kafuwa.

A ranar 15 ga watan Disamban shekarar 2021 ne, shugabannin kasashen Sin da Rasha suka gana da kafar bidiyo, inda suka sanar da fadada alakar dake tsakaninsu, yayin da cinikayya tsakanin sassan biyu da kai wani sabon matsayi.

Muhimman labarai 10 da suka faru a duniya a shekarar 2021 da CMG ya fitar_fororder_211229世界21049-hoto3

Kana a watan Agusta, dakarun Amurka da kawayenta suka fice daga kasar Afghanistan bayan shafe shekaru 20 a ckin kasar, kuma har yanzu kasar tana fuskantar kalubalen tsaro da tattalin arziki. A shekarar da muke shirin ban kwana, Amurka da Turai sun fuskanci hauhawar farashin kaya da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Muhimman labarai 10 da suka faru a duniya a shekarar 2021 da CMG ya fitar_fororder_211229世界21049-hoto2

Bugu da kari zaman tankiya ya karu, tsakanin Rasha da kungiyar tsaro ta NATO kan batun Ukraine. Kana a ranar 6 ga watan Janairu, masu bore dake goyon tsohon shugaban Amurka Donald Trump, sun kai hari a kan majalisar dokokin kasar, don neman a soke sakamakon zaben shugabancin kasar.

A shekarar ce kuma, Japan ta sanar da zubar da dagwalon ruwan tashar nukiliyar Fukoshima a cikin teku, matakin da ya gamu da fushin kasashen duniya.

Muna fatan samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, alheri da karuwar arziki a duniya baki daya a sabuwar shekarar 2022, Amin. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)