logo

HAUSA

Jawabin Shugaban CMG Na Murnar Sabuwar Shekara

2022-01-01 15:10:42 CRI

 

A ranar yau 1 ga watan Janairun shekarar 2022, shugaban babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG Mr. Shen Haixiong ya gabatar wa masu sauraron sassa daban daban na duniya jawabin murnar sabuwar shekara ta gidan telebijin na duniya na kasar Sin CGTN, da gidan rediyon kasar Sin CRI, da kuma yanar gizo.

Abokai masu sauraro:

Yau ranar ce ta farko ta sabuwar shekarar 2022. Shekarar 2022, shekara ce ta damisa bisa kalandar gargajiyar kasar Sin. Daga nan Beijing, ina muku murnar sabuwar shekarar damisa, kuma ina fatan cike kuke da kuzari a sabuwar shekara.

Jawabin Shugaban CMG Na Murnar Sabuwar Shekara_fororder_部长照片(内文用)

A shekarar 2021 da ta gabata, an cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Jam’iyyar ta kara mambobinta daga 50 da wani abu kawai yau shekaru 100 da suka wuce, zuwa fiye da miliyan 90 a yanzu. Tana kuma jagorantar al’ummun kasar wajen samun abun al’ajabi irin na kasar Sin.

A sabon zamani da muke ciki, a karkashin shugabancin Xi Jinping, an raya zaman al’umma mai matsakacin karfi a kasar Sin daga dukkan fannoni, tare da kawar da kangin talauci baki daya, wadda ta taba addabar Sinawa cikin dubban shekaru. A matsayinsa na mai rubuta bayanai, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, ya watsa shirye-shirye masu kayatarwa da dama, kamar “Kafa wata sabuwar kasar Sin”, “Yin gwagwarmaya don fita daga kangin talauci”, “Raya zaman al’umma mai matsakacin karfi a kasar Sin domin amfanin jama’a” da dai sauransu, wadanda suka bayyana yadda jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da jama’ar Sin suke yin gwagwarmaya, tare da yin wa kasashen duniya karin bayani kan ainihin dalilin da ya sa jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta rika samun ci gaba cikin shekaru 100 da suka wuce.

Yau wata guda da ya gabata, aka cika shekaru 80 da kasar Sin ta fara watsa shirye-shirye ga kasashen ketare. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga CMG, inda ya karfafa gwiwar ma’aikatan CMG, da mu bayyana labarun kasar Sin, da ra’ayin kasar ta hanyar da ta dace, a kokarin kafa wata muhimmiyar kafar yada labarai ta sabon salo a duniya, wadda ke da karfin ba da jagora, watsa shirye-shirye, da ba da tasiri. Ma’aikatan CMG za mu ci gaba da kokarinmu, don cimma wannan manufa.

Kamar yadda magabatan Sinawa kan ce, “wahala kan sa mutum gogewa, kamar yadda guga ke sa dutse santsi.” Sakamakon sauye-sauyen yanayin da ake ciki a shekaru 100 da suka gabata, da ma barkewar cutar COVID-19, ba a samu zaman lafiya yadda ya kamata a duniyarmu a yanzu ba. Amma burinmu na neman zaman lafiya, bunkasuwa, zama mai dadi ba zai tsaya ba. Shirye-shiryen da CMG ya tsara, kamar su “Kasar Sin Dake Cikin Tatsuniyoyi”, da “Kasar Sin Dake Cikin Kalaman Magabata”, da “Sunayen Garuruwan Sin”, da dai sauransu, dukkansu sun bayyana dogon tarihin Sin, da ma zaman rayuwar al’ummar Sin mai gaskiya da dadi. Haka kuma, shirye-shirye masu taken “Wuraren Yawon Shakatawa Na Sin”, da “Wasannin Olympics Dake Cikin Zane-zane” da “Kayayyakin Sassaka”, sun bayyana kyakkyawar kasar Sin da yadda Sinawa ke jin dadin wasannin motsa jiki a zamanin yau.

Bugu da kari, CMG ta watsa shirin bidiyon kai tsaye kan yadda ’yan sama-jannati suka ba da darasi a tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, lamarin da ya kara kwarin gwiwar matasa marasa lisaftuwa wajen gudanar da ayyukan binciken sararin samaniya a nan gaba. Game da batun yadda giwaye 16 na lardin Yunnan suka kashe rabin shekara suka kaura sa’an nan suka koma gida, tashar CGTN, da CMG Mobile, wato tashar watsa labarai ta yanar gizo ta CMG sun bibiyo labarin, har ma sun watsa shirye-shiryen bidiyo na kai tsaye har na tsawon awoyi fiye da 7000, lamarin da ya jawo hankulan duk duniya.

Gaskiya ita ce tushen aikin ’yan jarida. A wannan shekara, mun tsaya a kan wanzar da adalci bisa hakikanin gaskiyar al’amuran da suka faru. A game da jerin sunayen kasashen da suka yi fice wajen yaki da cutar Covid-19 da aka fitar, wanda bai dace da gaskiyar lamarin ba, mun gudanar da “binciken sauraron ra’ayoyin masu bibbiyar shafukan yanar gizo a fadin duniya” har sau uku, inda muka kai ga bayyana ainihin lamuran da suka faru, wanda ya samu karbuwa, da amincewa daga masu bibbiyar shafukan yanar gizo sama da miliyan dari a fadin duniya.

A rahotannin da muka bayar dangane da yanayin da ake ciki a kasar Afghanistan, hoton bidiyon da muka dauka daga kasar, ya tona sirrin yadda wasu kasashe ke nuna karfin tuwo yadda suka ga dama, da ma cin zarafin dan Adam. Za mu ci gaba da sauke nauyin da ke bisa wuyanmu, da yin kokarin bayyana gaskiyar lamuran dake faruwa a duniya. Da fatan takwarorinmu na kasashen yammaci ma za su kiyaye sunan ’yan jarida! Mu yi kokarin maido da gaskiyar da aka rufe, da moriyar siyasa, da kabilanci da nuna bambanci, mu yi kokarin sa kaimin samar da yanayi mai adalci ga aikin jarida a duniya.

Ba wani abu, ko da tsaunuka ko teku, da zai iya raba wadanda ke da kudurori da burika na bai daya. Cikin shekarar da ta gabata, kafar CMG ta yi ta kara kulla zumunta da abokai daga sassan duniya. Sama da sakwanni da wasiku 600 ne aka yi musaya tsakaninmu da takwarorinmu na kasa da kasa, baya ga ganawa sama da 20 da muka gudanar kai tsaye, ko kuma ta hoton bidiyo. Tare muka kafa tsarin hadin gwiwa mai kunshe da bangarori da dama, da kuma aminci da juna, kuma musayar da muka yi tare da takwarorinmu ta hau ta gada a tsakaninmu, a yayin da sakwannin da aka aiko mana sun karfafa mana gwiwa kara inganta aikinmu. Muna muku godiya!

Cikin wannan karnin da muke fuskantar da damammaki iri-iri, muna dukufa wajen yin kwaskwarima a fannin yada labarai. Game da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta birnin Tokyo, CMG ya cimma nasarar watsa shirye-shiryen gasar wasannin motsa jiki kai tsaye da fasahar 4K a tsakanin kasa da kasa a karo na farko, inda aka sami masu kallon shirye-shiryen sama da miliyan dari 4 cikin watanni uku. Bayan kwanaki sama da talatin kuma, za a sake kunna wutar gasar wasannin motsa jiki ta Olympics a birnin Beijing. A wannan karo ma, ta hanyar amfani da fasahohin 5G da 4K, da 8K da AI, CMG ya kafa dakunan watsa shirye-shirye kai tsaye, cikin jiragen kasa dake zuwa birnin Zhangjiakou daga birnin Beijing. Wannan ne karo na farko, da aka warware matsalar watsa shirye-shiryen bidiyo cikin jiragen kasa masu saurin gaske a duk fadin duniya. Kuma, muna maraba da dukkanin kafofin watsa labarai na kasashen duniya, da su yi amfani da wannan daki, domin watsa shirye-shirye masu kayatarwa, game da gasar Olympics ta lokacin sanyi ta birnin Beijing ga masu kallo na kasa da kasa.

Za mu shiga shekarar damisa bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, da fatan kowa zai kasance lami lafiya cikin sabuwar shekara. Haka kuma, cikin wannan sabuwar shekara, Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, za ta kira cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 20, domin tsara sabon shirin raya kasa. Mu ma za mu ci gaba da dukufa, da mai da matukar hankali kan ayyukanmu, domin sarrafa shirye-shirye masu ilmantarwa, da kuma kayatarwa, yayin da muke yiwa jama’ar kasashen duniya harkokin dake faruwa a kasar Sin bisa fannoni daban daban, ta yadda za mu ba da gudummawa tamu wajen karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama.

Ina muku fatan alheri, da ma duniyar mu fatan alheri!