logo

HAUSA

Kafar CMG ta kafa tashar watsa shirye-shirye kai tsaye jiragen kasa masu sauri

2022-01-06 15:36:10 CRI

Kafar CMG ta kafa tashar watsa shirye-shirye kai tsaye jiragen kasa masu sauri_fororder_0106-CMG-Faeza

Watsa ingantattun bidiyo kai tsaye daga jirgin kasa mai saurin tafiyar kilomita 350 kan kowace sa’a, ba abu ne mai sauki ba, sai dai, babban rukunin gidan talabijin da rediyo na kasar Sin CMG, ba ya kasa a gwiwa wajen tunkarar kalubale.

CMG ya kaddamar da wata sabuwar tashar watsa shirye-shirye kai tsaye irin na zamani a jirgin kasa mai saurin tafiya da ya hada babban birnin Beijing da Zhangjiakou, da zai karbi bakuncin wasannin Olympic, lamarin da ya nuna yadda kasar ke mayar da hankali kan fasahar zamani a bangarori daban-daban. (Faeza Mustapha)