logo

HAUSA

Amurka Ce Ta Gudanar Da Harkokin Diplomasiyya Ta Hanyar Yin Barazana

2022-01-12 21:55:32 CRI

Kwanan baya, jami’an kasar Amurka sun ayyana matakin da kasar Sin ta dauka domin mayar martani kan kasar Lithuania, a matsayin barazana. Lalle Amurka tana mara wa mahukuntan Lithuania baya ne domin dalilan siyasa, a yunkurin dalike ci gaban kasar Sin bisa hujjar fakewa da batun Taiwan. Abin da Amurka ta yi ya nuna yadda take yin danniya a akasarin ra’ayoyin jama’a na kasa da kasa,

Sin da Lithuania sun gamu da matsala wajen raya huldar da ke tsakaninsu. Shin wa zai dauki alhakin lamarin? Gwamnatin Lithuania dai ta ci amana, ta saba ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”. Kasashen duniya ba su amince da abin da ta yi ba. Amma Amurka ta ayyana matakin da kasar Sin ta dauka domin kiyaye ikon mulkin kasa a matsayin wani irin barazana. Wai kura ce za ta cewa kare maye.

Waiwaye adon tafiya. Amurka ce ta kirkiro diplomasiyyar yin barazana. A shekaru da dama da suka wuce, Amurka ta ba da misali da yawa ta hanyar daukar matakai masu yawa.

Wa ke yi wa kasashen duniya barazana? Wa ke barnata tsari da odar kasa da kasa da ka’idojin da ke tsakanin bangarori daban daban? Kasashen duniya sun san haka sosai. Amurka ba za ta iya karfafa karfinta ta hanyar yiwa wasu kasashe barazana, hakika, a karshe ba za ta yi nasara ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan