Kasar Sin ta karyata zargin da Amurka da EU suka yi game da halastaccen matakin da ta dauka na kare ‘yancinta kan Lithuania
2021-08-13 21:05:47 CRI
A yau ne, kasar Sin ta karyata zargin da Amurka da kungiyar Tarayyar Turai (EU) suka yi mata, kan halastaccen mataki na baya-bayan da ta dauka kan kasar Lithuania. Tana mai cewa, wasu kasashe da daidaikun mutane suna yaudarar jama’a kan wannan batu.
A ranar Talata ce, kasar Sin ta sanar da yanke shawarar kirawo jakadanta dake kasar Lithuania, ta kuma bukaci gwamnatin Lithuania da ita ma ta janye nata jakadan dake kasar Sin, tana mai cewa, shawarar Lithuania ta barin mahukuntan yankin Taiwan na kasar Sin, su bude ofishin wakilci, da sunan Taiwan, ya saba manufar kasar Sin daya tak a duniya.
Da take karin haske kan wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, bangaren Sin, yana adawa da babbar murya kan zargin da Amurka ke yiwa matakin na kasar Sin, ta kuma bukaci EU, da ta daina aikewa da mummunan sako kan batun da ya shafi moriyar kasar Sin ko haddasa wata sabuwar matsala a alakar Sin da EU. (Ibrahim)
Labarai Masu Nasaba
- Kasar Sin Tana Goyon Bayan Aikin Binciken Gano Asalin COVID-19 Da WHO Ke Yi Amma Tana Adawa Da Yadda Ake Siyasantar Da Batun
- Kasar Sin ba ta cikin hadarin barkewar COVID-19
- Labarin wani saurayin kasar Sin, wanda ke gudanar da aikin injiniya a Najeriya
- Sin ta yabawa kokarin mahukuntan Pakistan game da bincike da suke yi don gane da harin ta’addanci na Dasu