logo

HAUSA

Kungiyar PACJA na shirin samar da wani tsari na kakkabe fatara ta hanyar fadada amfani da makamashi mai tsafta

2021-12-16 11:14:23 CRI

Kungiyar PACJA na shirin samar da wani tsari na kakkabe fatara ta hanyar fadada amfani da makamashi mai tsafta_fororder_光伏

Kungiyar PACJA mai rajin ingiza manufar amfani da makamashi mai tsafta, mai hedkwata a birnin Nairobin kasar Kenya, ta kaddamar da wani shiri na yayata damar amfani da makamashi mai tsafta a Afirka, a wani bangare na ayyukan ta na sauya akalar nahiyar Afirka zuwa amfani da nau’o’in sabbin makamashi.

Cikin wata sanarwar da ya fitar a Nairobi, babban daraktan kungiyar ta PACJA, Mr. Mithika Mwenda, ya ce shirin na hadin gwiwa ne tare da cibiyar kwararru a fannin kare yanayi ta “Germanwatch”, mai hedkwata a birnin Bonn na kasar Jamus, wanda ke da nufin warware matsalolin talauci mai nasaba da amfani da makamashi a Afirka.

Mwenda ya kara da cewa, shirin zai baiwa kungiyoyin gama kai horo, na dabarun bunkasa manufofi da za su ba da damar samun isasshen makamashi da ake isa sabuntawa a sassan Afirka.

Ya ce, shirin mai lakabin "Tabbatar da manufofi masu mai da hankali ga al’umma a fannin samar da makamashi mai tsafta, ta hanyar kungiyoyin gama kai" zai warware matsalar samar da manufofi, da dokoki, da kudaden gudanarwa, wadanda ke zama kalubale dake dakile damar samun isasshen makamashi mai tsafta a Afirka.  (Saminu)

Saminu