logo

HAUSA

Kasar Sin za ta gaggauta samar da rigakafin cutar COVID-19 ga kasashen Afirka

2021-12-14 10:47:18 CMG

Kasar Sin za ta gaggauta samar da rigakafin cutar COVID-19 ga kasashen Afirka_fororder_1214-Sin-Afirka-rigakafi-bello-1

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, mista Wang Wenbin, ya bayyana a jiya Litinin cewa, kasar Sin za ta gaggauta samar da tallafin rigakafin cutar COVID-19 ga kasashen Afirka, don taimakawa ganin bayan annobar a nahiyar Afirka.

A cewar mista Wang, kasar Sin za ta samar da karin alluran riga kafi biliyan 1 ga nahiyar Afirka, matakin dake cikin manufar kasar ta karfafa hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a fannin dakile annoba, da taimakawa kasashen wajen magance “gibin karbar alluran rigakafi”.

Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara kokarin hadin kai, da sada zumunta tare da kasashen Afirka, da aiwatar da sakamakon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, da kara saurin ba da tallafin riga kafin cutar COVID-19 ga nahiyar Afirka, don taimakawa al’ummun Afirka samun alluran riga kafin masu rahusa, da ganin bayan annobar a karshe. (Bello Wang)

Bello