logo

HAUSA

WHO: Matakan Dakile COVID-19 A Gasar Wasannin Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Beijing Suna Da Karfi

2022-01-09 20:49:02 CRI

Wani babban jami’in hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce, shirin da gwamnatin birnin Beijing ta yi don tabbatar da dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 a yayin gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022 a wata mai zuwa yana da karfin gaske.

A cewar jaridar Lianhe Zaobao ta harshen Sinanci ta kasar Singapore, daraktan sashen ayyukan gaggawa na hukumar WHO, Michael Ryan, ya yi wannan tsokaci ne a taron manema labarai a ranar Alhamis, inda ya nuna cewa, hukumar tana aiki da kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa IOC domin samar da shawarwarin fasaha game da yadda za a karbi bakuncin gasar yadda ya kamata.

An jiyo Michael Ryan yana cewa, hukumomin kasar Sin sun dauki tsauraran matakai, kuma sun fitar da jerin littattafan ba da jagora daban daban game da batutuwan dake shafar yaki da annobar.

Ya kara da cewa, yana da kwarin gwiwa bisa ga bayanan da ake da su cewa, matakan da kasar Sin take dauka kawo yanzu game da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022 suna da matukar tsauri kuma suna da matukar karfi, kuma a halin yanzu, babu wata karuwar barazanar yaduwar cutar.(Ahmad)

Ahmad