logo

HAUSA

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Kamaru ya yi watsi da batun siyasantar da wasannin motsa jiki

2021-12-31 12:20:48 CRI

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Kamaru ya yi watsi da batun siyasantar da wasannin motsa jiki_fororder_冬奥

Shugaban kwamitin kula da harkokin wasannin Olympics na kasar Kamaru kanar Hamad Kalkaba Malboum, ya zanta da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a birnin Yaounde, babban birnin kasar Kamaru a ranar 29 ga wata, inda ya bayyana cewa, bai amince da siyasantar da wasannin motsa jiki da wasu kasashe suke yi ba, kana yana ganin cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing za ta samu nasara.

Kanar Malboum ya kara da cewa, babu batun bambancin kabilu, da al’adu, da ma yaruka a harkar wasannin motsa jiki, kuma wasanni na taimakawa wajen kau da rikice-rikice, da sada zumunta, da shimfida zaman lafiya. Don haka ya kamata a nuna rashin yarda da sanya batutuwan siyasa a cikin wasannin motsa jiki.

Haka kuma ya nuna cewa, ko da yake kasar Kamaru tana yanki mai zafi, amma gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na jawo hankalin al’ummar kasar sosai, kasancewarta wata gagarumar gasar wasannin motsa jiki ta duniya a lokacin hunturu.

Kanar Malboum yana ganin cewa, cutar COVID-19 na yaduwa a duk duniya, kuma shirya gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi a wannan lokacin musamman zai nuna ruhin motsa jiki na yin namijin kokari ba tare da kasala ba, lamarin da zai kara kwarin gwiwar duniya wajen yaki da cutar. (Kande Gao)