logo

HAUSA

Mene ne sirrin dakunan wasannin Olympics na Beijing?

2021-12-31 17:00:43 CRI

Mene ne sirrin dakunan wasannin Olympics na Beijing?_fororder_冰丝带

Dakunan wasannin Olympics, ana amfani da su sosai a yayin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi, amma a kan fuskanci matsalolin kashe yawan kudade wajen kiyaye su, da ma gaza amfani da su kullum. Don haka yadda za a rika amfani da dakunan ya zama wani muhimmin batu da kasashe masu karbar bakuncin gasar Olympics ke bukatar warwarewa.

A matsayinsa na birnin farko, da ya taba samun damar shirya gasar Olympics sau biyu, yadda birnin Beijing ya yi amfani da dakunan wasannin Olympics na shekarar 2008 ya jawo hankalin mutane sosai, yayin da yake shirya wannan gasar Olympics ta lokacin sanyi.

Za a yi dukkan gasannin kankara a birnin Beijing, ban da dakin wasannin gudun kankara da wani dandamalin wasannin tsalle daga koli a kan dusar kankara, su sabo ne da aka gina su, sauran dakunan wasannin kuwa an gina su ne a gasar wasannin Olympcis ta lokacin zafi.

Bugu da kari kuma, bayan gasar, za a yi amfani da wadannan dakunan wajen kyautata zaman rayuwar jama’a. Dumbin mazauna birnin ba za su zauna a gida a lokacin hunturau ba, a maimakon haka, za su rika shiga wasu wasannin motsa jiki na lokacin sanyi a wuraren. (Kande Gao)