logo

HAUSA

An kaddamar da bikin nuna al’adun Olympics a Beijing

2022-01-07 14:42:38 CMG

An kaddamar da bikin nuna al’adun Olympics a Beijing_fororder_220107-B3-OLYMPCS

A jiya Alhamis, aka kaddamar da bikin nuna al’adun wasannin Olympics, mai taken “haduwa da juna a birnin Beijing”, da kuma bikin nuna fasahohin al’adu na kasashen duniya mai take iri daya, duk a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Za a yi amfani da bukukuwan wajen wayar da kan jama’a, game da ilimin wasannin Olympics na lokacin hunturu, da nau’in wasannin na nakasassu, wadanda za a gudanar da su a birnin Beijing

Ana gudanar da bikin na nuna fasahohin al’adu na kasashe daban daban ne a wani wuri da ke birnin Beijing, gami da kafar intanet, inda za a iya morewa da nune-nune kusan dari daya, wadanda ke wakiltar al’adu na kasashe da yankuna 22.

Ta wannan hanya, ana neman samar da wani yanayi mai armashi kafin a kaddamar da wasannin Olympics, da nuna wani yanayi na musamman da birnin Beijing ke da shi, wanda ya kasance wani birni na farko a duniya, da ya samu damar karbar bakuncin wasannin Olympics na lokacin zafi da na hunturu. (Bello Wang)

Bello