logo

HAUSA

Akwai bukatar dakatar da yi wa matan da take son daukar ciki da masu shayarwa alluran rigakafin COVID-19?

2022-01-04 08:29:18 CRI

Akwai bukatar dakatar da yi wa matan da take son daukar ciki da masu shayarwa alluran rigakafin COVID-19?_fororder_u=3455268282,1649590465&fm=26&fmt=auto(1)

Yanzu haka ana kokarin yi wa al’umma alluran rigakafin cutar numfashi ta COVID-19 a sassa daban daban a duniya, don ganin bayan cutar cikin hanzari. An hana a yi wa masu juna biyu alluran. To, Akwai bukatar dakatar da yi wa matan da suke son daukar ciki da masu shayarwa alluran rigakafin COVID-19? Masanan ilmin allurar rigakafin cututtuka na kasar Sin sun ba mu amsa.

Alluran rigakafin cutar COVID-19 da ake yi wa al’umma suna da inganci kuma ba su lahanta lafiyar mutane, don haka wajibi ne maza da mata wadanda suke neman haihuwa su bari a yi musu alluran. Idan bayan da aka yi wa matan alluran, sun gano cewa, lalle sun samu ciki, babu bukatar su dauki wasu matakai na musamman na likitanci, wadanda suka hada da zub da ciki ta wasu hanyoyi. An cimma daidaito kan lamarin a sassa daban daban na duniya.

Masanan kasar Sin sun yi nuni da cewa, an yi taka-tsantsan kan dakatar da yi wa masu juna biyu alluran. Ya zuwa yanzu dai ba a gano munanan abubuwan da suka abku kan masu juna biyu ko kuma ‘yan tayinsu sakamakon allurar rigakafin cutar COVID-19 ba, amma za a ci gaba da sa ido kan wannan fanni.

Kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya na kasar Sin ya yi bayani da cewa, ko da yake ya zuwa yanzu babu bayanai kan illar da alluran rigakafin COVID-19 ke kawo wa kananan yaran da suke shan nono, amma zai fi kyau likitoci mata da nas-nas mata da matan da suke fuskantar babbar barazanar kamuwa da cutar COVID-19 su karbi alluran. Haka kuma shayarwa yana da muhimmanci sosai ga lafiyar kananan yara, don haka, kamar yadda aka saba yi a baya a kasashen duniya, an bai wa masu shayarwa shawarar ci gaba da shayar da jarirai nonon uwa zalla bayan da aka yi musu alluran.

Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana bayani da cewa, dalilin da ya sa ake yin allurar rigakafin cututtuka shi ne domin kare mutane daga kamuwa da cuta, da kare su daga kasancewa cikin halin gobe da nisa, da kuma dakile yaduwar cututtuka, a kokarin kiwon lafiyar yawancin mutane. Kamata ya yi kowa da kowa ya je a yi masa allura, ta haka za a ba da kariya ga al’umma baki daya. Yawan mutanen da aka yi musu alluran yanw karuwa, sai ana kara ba da kariya mai kyau ga al’umma. Wajibi ne a yi allura cikin hanzari. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan