logo

HAUSA

Sharhi: Wanda Ke Samar Da Gudummumawa A Lokacin Da Kake Bukata Shi Ne Aminiyarka Ta Ainihi

2021-10-03 18:40:21 CMG

Sharhi: Wanda Ke Samar Da Gudummumawa A Lokacin Da Kake Bukata Shi Ne Aminiyarka Ta Ainihi_fororder_微信图片_20211003183903

A watan Satumban bana, alluran rigakafin cutar Covid-19 kimanin miliyan 95 da shirin Covax ya samar suka isa kasashen Afirka, wadanda suka zama mafi yawa da kasashen Afirka suka karba cikin wata guda. Sai dai a kwanan nan, shirin na Covax ya sanar da cewa, zai rage alluran kimanin miliyan 150 da ya yi shirin samarwa kasashen Afirka cikin wannan shekara. An kuma yi hasashen ya zuwa karshen wannan shekara, alluran rigakafin da shirin zai iya samar wa kasashen Afirka zai kai kimanin miliyan 470, wadanda za su iya biyan bukatun kaso 17% na al’ummar Afirka kadai.

Ya zuwa yanzu, al’ummar kasashen Afirka miliyan 50 ne kadai aka yi wa rigakafin, wadanda suka dau kaso 3.6% na al’ummar kasashen Afirka baki daya, a yayin da adadin ya kai 65% a kasar Amurka da ma sama da 60% a kasashen tarayyar Turai.

A game da wannan, Matshidiso Moeti, darektar hukumar lafiya ta duniya mai kula da harkokin Afirka ta bayyana cewa, yadda aka sanya haramcin fitar da rigakafin zuwa ketare da ma tara su fiye da kima ya kawo cikas ga aikin samar da rigakafin ga kasashen Afirka. Sai dai rashin daidaiton samar da rigakafin a sassan duniya zai iya sa kasashen Afirka da ke karancin samun rigakafin su zama sassan da ake yawan samun sauye-sauyen cutar.

Faduwa ta zo daidai da zama, inda a kwanan baya kasar Sin ta sanar da matakan tallafa wa kasashe masu tasowa wajen rigakafin cutar. A kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin muhawarar babban taron MDD karo na 76 ta yanar gizo, inda ya sanar da cewa, kasar Sin za ta yi iyakacin kokarin samar da alluran rigakafi biliyan 2 ga kasashen ketare a cikin wannan shekara, kuma baya ga samar da gudummawar dala miliyan 100 ga shirin Covax, za ta kuma kara samar da rigakafin miliyan 100 ga kasashe masu tasowa cikin wannan shekara. Kawo yanzu kuma, kasar Sin ta riga ta samar da rigakafin biliyan 1.2 ga kasashe da kungiyoyin duniya sama da 100, inda har ta zama ta farko a duniya wajen samar da gudummawar rigakafin, matakin da kuma ya samu yabo daga MDD da ma kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka.

John Nkengasong, darektan cibiyar kandagarkin cututtuka ta Afirka ya bayyana godiya ga kasar Sin bisa gudummawar da ta samar wa kasashen Afirka. Sai kuma Teodoro Obiang Nguema Mbasogo shugaban kasar Equatorial Guinea da ya tabbatar da amincin rigakafin da kasar Sin ta samar bayan an yi masa allurar, yana mai yabawa kasar Sin bisa gudummawar da ta samar, tare da bayyana kasar Sin a matsayin babbar aminiyar kasarsa.

A nasu bangaren, kasashen yamma da suke bayyana kansu a matsayin kasashen da ke jagorantar aikin kandagarkin cutar a duniya, kansu kadai suke bai wa kansu fifiko wajen raba rigakafin tare da tara su fiye da yadda suke bukata.

Kwanan baya, tsohon firaministan kasar Burtaniya, Gordon Brown ya wallafa wani bayani ta jaridar the Guardian, inda ya soki kasashen yammacin duniya bisa ga yadda suke yawan tara alluran rigakafin. Ya ce, nan ba da jimawa ba, rigakafin da za a samar a fadin duniya zai kai biliyan 10, adadin da zai kai biliyan 27 a watan Yunin shekara mai zuwa, wadanda za su ishi dukkanin al’ummar duniya, har su samu guda biyu kowanensu. Sai dai abin da ke faruwa shi ne, zuwa lokacin zafi na shekara mai zuwa, sama da rabinsu za su kasa samun damar yin rigakafin.

A yayin da ake fuskantar annobar Covid-19, ba wanda zai iya samun kariya muddin dai kowa bai samu kariya ba. Sanin kowa ne cewa, taimaka wa kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa wajen samun rigakafi cikin adalci, zai amfanawa duniya baki daya, sai dai kasashen yammacin duniya da kasar Sin, sun bambanta a matakan da suke dauka. Tun da farko, kasar Sin ta sanar da samar da rigakafin a matsayin kayan da zai amfanawa kowa a duniya, haka kuma ta yi ta kokarin samar da gudummawa ga kasashe masu tasowa. Sinawa kan ce, “zumunci yana tabbata ne a lokacin wahala”, lalle kasashe masu tasowa ma sun fahimci wace ce aminiyarsu.(Lubabatu)

Lubabatu