logo

HAUSA

Sin za ta samar da karin rigakafi ga kasashe masu tasowa

2021-11-12 20:23:35 CRI

Sin za ta samar da karin rigakafi ga kasashe masu tasowa_fororder_161136980227005800_a700xH

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da rungumar manufar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ta fuskar kiwon lafiya, ta hanyar aiwatar da matakai daki daki, ciki har da samar da tallafin kyauta ga kasashe masu tasowa, ta yadda za su samu karin rigakafin COVID-19.

Wang, wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce Sin za ta ba da gagarumar gudummawa wajen samar da rigakafi ga dukkanin sassa, tare da tallafawa daukacin yakin da ake yi da annobar COVID-19 cikin gaggawa.

Wani rahoto na rukunin masana ya nuna cewa, ya zuwa karshen watan Oktoba, an yi alluran rigakafi sama da biliyan 7 a fadin duniya baki daya. Rahoton na “Economist” ya ce, Sin na kan gaba wajen samar da rigakafi, inda adadin rigakafin da Sin din ta samar aka kuma yiwa al’ummar kasar Chile ya kai kaso 79%, yayin da na Cambodia ya kai 77%, adadin da ya haura adadin wanda aka yiwa al’ummun dake kasashe masu ci gaba kamar Amurka da Turai. (Saminu)