logo

HAUSA

Hukumar lura da bunkasa harkokin zuba jari ta jihar Kano ta bullo da tsare-tsaren tallafawa ’yan kasuwar kasar Sin wajen zuba jari a Jihar

2022-12-31 17:05:31 CMG Hausa

A ranar Juma’a 30 ga wata ne wani rukunin ’yan kasuwar kasar Sin suka ziyarci hukumar lura da bunkasa harkokin zuba jari ta jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya inda suka nuna sha’awar su ta kafa masana’antar yin siminti a jihar.

Tawagar ’yan kasuwar na karkashin jagorancin manajan daraktan kamfanin UBM Nigeria Limited Mr. Ru Changyu wanda suka zo daga jamhuriyyar Nijar.

A lokacin da take karbar ’yan kasuwar, darakta janaral ta hukumar Hajiya Hama Aware ta ce, gwamnatin jihar Kano ta tanadi dukkan mahimman abubuwa da za su kwadaitar da masu zuba jari sha’awar saka jarinsu a jihar.

Hajiya Hama Aware ta tabbatarwa ’yan kasuwar cewa gwamnatin Kano za ta samar musu da mahimman bayanai da duk wani agajin da ya kamata domin su samu saukin assasa wannan kamfani.

Da yake nasa jawabin, jagoran ayarin Mr. Ru Changyu ya ce sun ziyarci hukumar ne domin samun bayanai da goyon baya a kan yadda za su kafa kamfanin siminti a Kano.

Ya ce yanzu haka suna da kamfanin samar da kayan gine-gine a garin Tawa dake jamhuriyyar Nijar, sannan yanzu suna son samar da kamfanin siminti a jihar ta Kano inda za su rinka shigo da sinadaran aikin daga Nijar.

Daga karshe ya yi fatan cewa gwamnatin jihar Kano za ta ba su hadin kai da goyon bayan da ya kamata domin tabbatar da ganin sun cimma wanann buri nasu. (Garba Abdullahi Bagwai)