Sin Ta Gudanar Da Tsarin Jigilar Ruwa Dake Amfanawa Jama’a
2022-12-30 20:05:37 CMG HAUSA
Daga MINA
Abokai, ranar 27 ga watan Disamba na bana ne aka cika shekaru 20 da Sin ta aiwatar da tsarin jigilar ruwa daga kudu zuwa arewacin kasar. Gwamnatin Sin ta gudanar da wannan tsari domin daidaita matsalar karancin ruwa da sassan arewacin kasar ke fuskanta. Wannan tsari yana jigilar ruwan kogin Yangtse dake tsakiyar kasar Sin, wanda ya kasance kogi mafi tsayi a kasar, zuwa wuraren dake fama da karancin ruwa na arewacin kasar,ciki hadda Beijing da Tianjin da sauransu. An fara gina shi a ran 27 ga watan Disamba na shekarar 2002.
Tun lokacin da aka kammala gina sashin gabas da na tsakiya na wannan aiki a shekarar 2014 zuwa yanzu, an yi jigilar ruwan da yawansa ya kai cubic mita biliyan 58, tsarin dake amfanawa jama’a da yawansu ya kai miliyan 150 na gundumomi fiye da 280 na birane 42. Ban da wannan kuma, tsarin ya kawowa wadannan wurare babban moriya ta fannin tattalin arziki da kare muhalli.
Aiwatar da wannan tsari na da wuya matuka, amma gwamnatin Sin ta kammala shi wanda ya kasance daya daga cikin ayyuka mafi ban mamaki a duniya, duk bisa manufar “Jama’a gaba da komai”.
Jama’ar dake Beijing da Tianjin da dai sauran wurare a arewacin kasar, wadanda da ma suka dogara da ruwa daga kasa, yanzu suna amfani da ruwa mai tsabta da aka yi jigila daga kudancin kasar, ba tare da damuwa da matsalar ruwa ba. (Mai zana da rubuta: MINA)