An Ayyana Ranaikun Bude Manyan Tarukan Siyasa Na Kasar Sin Na Shekarar 2023
2022-12-30 18:21:05 CMG HAUSA
A yau Juma’a ne kwamitin dindindin na majalissar wakilan jama’ar kasar Sin ko NPC na 13, ya amince da ayyana ranaikun bude manyan tarukan siyasa biyu na kasar Sin, wato taron shekara-shekara na majalissar wakilan jama’a na kasar karo na 14, wanda za a bude a ranar 5 ga watan Maris din shekarar 2023 dake tafe a birnin Beijing, da kuma zaman taro na farko, na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC ta 14, wanda ake fatan budewa a ranar 4 ga watan Maris na shekarar ta 2023 a birnin Beijing. (Saminu Alhassan)