logo

HAUSA

Shuagaban kasar Sin zai gabatar da jawabin maraba da sabuwar shekarar 2023

2022-12-30 11:17:36 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da jawabin maraba da sabuwar shekarar 2023, da karfe 7 na yammacin gobe Asabar, agogon Beijing.

Za a watsa jawabin nasa a manyan tashoshin talabijin da rediyo na CMG da shafukan yanar gizo da na kafofin sadarwa na zamani na manyan kafofin watsa labarai na kasar. (Fa’iza Mustapha)