logo

HAUSA

Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Sayarwa Yankin Taiwan Makamai

2022-12-30 21:15:51 CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce gwamnatin Sin ta bukaci Amurka da ta dakatar da sayarwa yankin Taiwan makamai, da kulla duk wata kwangila da ta shafi ayyukan soji da tsibirin na kasar Sin. Kaza lika Sin din na fatan Amurka za ta kaucewa kirkiro sabbin dalilai, wadanda za su haifar da zaman dar dar a zirin Taiwan.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa, game da amincewar baya-bayan nan da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi, da bukatar sayarwa Taiwan makamai, yayin taron manema labarai da ya gudana a yau Juma’a, Wang ya ce Sin za ta yi tsayin daka wajen kare ‘yancin mulkin kai, da tsaro, da moriyar ta. Jami’in ya kuma jaddada cewa, har kullum Sin na adawa da matakan Amurka na sayarwa yankin Taiwan na Sin makamai.

Bugu da kari, Wang ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta martaba manufar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyin hadin gwiwar nan guda uku da sassan biyu suka amincewa, kuma Amurka ta yi aiki bisa gaskiya, kan alkawarin da gwamnatin kasar ta yi na kin goyon bayan neman ‘yancin kan Taiwan.  (Saminu Alhassan)