logo

HAUSA

Lardunan kasar Sin suna bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka

2022-12-30 10:59:42 CMG Hausa

Yayin da watanni shida suka rage a gudanar da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na kasar Sin da Afirka na gaba, tawagar tattalin arziki da cinikayya daga lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, ta kammala rangadin da take yi a tsakiyar watan Disamba a wasu kasashen Afirka, a kokarin yayata bikin baje kolin a kasashen nahiyar.

A cewar hukumomin kasar, za a gudanar da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na kasar Sin karo na uku a watan Yuni mai zuwa, a birnin Changsha na lardin Hunan. A kokarin na ake yi na ganin an zurfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da kasuwanci da Afirka, tawagar da sashen kasuwanci na gwamnatin lardin sun ziyarci kasashen Mozambique, da Tanzania da Madagascar daga ranar 10 zuwa 21 ga watan Disamba.

Shugaban hukumar kwastan dake Changsha Zhu Guangyao ya bayyana cewa, a cikin ’yan shekaru kalilan, lardin Hunan ya zama daya daga cikin lardunan da suka fi yin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya da Afirka.

Godiya ga manufar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje, galibin lardunan kasar Sin ciki har da Hunan, sun yi amfani da damar da suke da ita, wajen shiga a dama da su don amfana da fifikonsu, kuma sun taka rawar gani kasancewarsu na farko a fannin yin cinikayya da Afirka.

Ga misali, alkaluman kididdigar ma’aikatar cinikayya ta lardin Zhejiang sun nuna cewa, lardin wanda ke kan gaba a fannin kasuwancin waje a kasar Sin, darajar cinikayyarsa da Afirka ta kai Yuan biliyan 235.7 a shekarar 2020, wanda ya kai kashi 18.2 bisa 100 na adadin cinikayyar kasar. (Ibrahim Yaya)