Xi: Sin da duniya cikin iyali daya suke
2022-12-29 14:03:43 CMG Hausa
A cikin jawaban murnar sabuwar shekarar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan waiwayi sakamakon da kasarsa ta samu kan harkokin wajen kasar, tare kuma da bayyana fatansa kan kyakkyawar huldar dake tsakanin Sin da sauran kasashen duniya, inda ya kan yi cikakken bayani kan manufofin tafiyar da harkokin kasar Sin da dabarun kasar kan yadda take daidaita matsalolin da duk duniya ke fuskantar. Daga jawabansa, ana iya gano cewa, Sin tana rungumar duniya ba tare da rufa rufa ba karkashin jagorancin shugaban kasar mai hikima.
A sabuwar shekarar 2023 dake tafe, kasar Sin za ta ingiza farfadowar al’ummar Sinawa bisa zamanintarwa irin ta kasar, kuma za ta yi kokari tare da sauran kasashen duniya domin wanzar da zaman lafiya da tabbatar da burin hada kai da samun bunkasuwa, ta yadda za a gina kyakkyawar makomar bil adama ta bai daya. (Jamila)