Wang Wenbin: Manufar Kasar Sin Ta Fifita Kare Rayukan Jama’a Ba Ta Sauya Ba
2022-12-29 18:50:03 CMG HAUSA
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce cikin shekaru 3 da suka gabata, kasar Sin ta rika sauya matakan da take aiwatarwa na kandagarki da shawo kan annobar COVID-19 bisa halin da ake ciki, amma duk da sauye-sauyen da aka samu, manufar kasar ta fifita kare al’umma, da tsaron rayukan su ba ta sauya ba.
Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a Alhamis din nan, ya ce wasu kafafen watsa labarai na yammacin duniya na ta cewa, wai sauyin matakan da Sin ta fara aiwatarwa a baya-bayan nan na nuna sauyin manufa ne, kuma hakan na nufin gwamnatin Sin ta canza matsaya, game da muhimmancin da take dorawa wajen mayar da jama’a gaban komai. Wang Wenbin ya ce irin wannan zargi ya sabawa gaskiya, da shaidu na kimiyya, kuma ana furta su ne kawai da wata mummunar manufa.
Kaza lika, Wang Wenbin ya ce tun bayan barkewar annobar, Sin ta ci gaba da mayar da aikin kare rayukan jama’a gaban komai, ta kuma yi duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da lafiyar al’umma, kana an yi duk abun da ya dace, don samar da jinya ga masu bukata. Har ila yau, cikin matakan yaki da wannan annoba, Sin ta ci gaba da tsara matakai daban daban, na kandagarki da shawo kan cutar tare da sauran muhimman ayyukan raya tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’umma yadda ya kamata. Har ila yau, gwamnatin kasar ta ci gaba da daidaitawa, da kyautata matakan kandagarki da shawo kan cutar bisa yanayin da ake ciki. (Saminu Alhassan)