Xi: Ina kula da damuwar al’ummar kasar Sin a ko da yaushe
2022-12-29 13:59:35 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara gabatar da jawabin taya murnar sabuwar shekara tun daga shekarar 2014, a cikin shekaru 9 da suka gabata, ya saba da waiwayen sabbin sauye-sauyen da suka faru a fadin kasar Sin, kuma ya kan yi fatan alheri ga ci gaban kasar. A cikin jawabai da ya gabatar, abu mafi jan hankalin jama’a shi ne kulawarsa kan rayuwar al’ummar Sinawa, alal misali bayar da ilmi ga yara, da yadda ake kulawa da tsoffafi, da hidimar kiwon lafiya ga majinyata, da kudin shigar manoman kasar da sauransu. (Jamila)