Ya kamata kasa da kasa su dauki matakai iri daya na magance yaduwar cutar COVID-19 ga dukkan jama’ar kasashen duniya
2022-12-29 20:24:45 CMG Hausa
Bayan da kasar Sin ta kyautata matakan yaki da cutar COVID-19, wasu kasashe sun sanar da matakan yiwa Sinawa dake da niyyar shiga kasashen gwajin cutar, ko da yake akwai wasu kasashe da dama dake bayyana cewa, ba za su sauya tsarin su domin yiwa Sinawa dake son shiga kasashen gwaji ba.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, ya kamata kasa da kasa su dauki matakai masu dacewa, da nuna ra’ayi iri daya ga dukkan jama’ar kasashen duniya, kuma bai kamata a haifar da illa ga mu’amala, da hadin gwiwa a tsakanin jama’ar kasashen duniya ba. (Zainab)