logo

HAUSA

Aikin agaji na Dandelion yana kula da mata da yara

2023-01-02 19:38:51 CRI

Kungiyar mata ta jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta fara aiwatar da aikin ba da hidima kan kiyaye ikon mata da yara mai suna "Dandelion" a shekarar 2017. Nan da shekaru shida da suka gabata, wannan aikin a yanzu ya zama wata alama ta kananan ayyukan agaji wanda ke da halayen kungiyar mata, da amfanar iyalai, kuma samun karbuwa daga wajen mazauna wurin. Ta hanyar samar da hidima ga mata, yara da iyalai a fannonin daidaita harkokin iyali, kare kai na yara, sanar da doka, da kula da hankali da dai sauransu, aikin na iya taimaka wa iyalai da yawa su magance matsalolin dake damu su, kana ya sanya mata su ji kulawa da suka samu daga gwamnati, su kara sanya mata da iyalai su ji dadi da tsaro, lallai wannan "Karamin aiki" na taka "babbar" rawar wajen kiyaye zaman jituwar iyali da kwanciyar hankali na zamantakewa.

Wei Yunling, tsohuwar shugabar sashen kare hakki da muradu na kungiyar mata ta Mongoliya ta gida, ta gaya mana cewa, Dandelion shi ne tsire-tsire da a kan iya samu a ko da yaushe a ciyawa. Akwai kwallon gashi mai launin fari a kan 'ya'yansa, kuma idan iska ta kada, sai ta yi birgima a hankali ta ko'ina, ta haka za ta haifar da sabuwar rayuwa a sabbin wurare. Lokacin da suka sanya sunan aikinsu, sun yi tunani da Dandelion. Ko da yake aikin din karami ne, amma suna fatan dukkan kananan ayyukan da suka yi, za su iya yaduwa da samun gindin zama a cikin zukatan yaran dake zaune ciyawa kamar yadda Dandelion yake.

Sun Lan ita ce daya daga cikin rukunin farko na malaman sa kai na aikin "Dandelion" a gundumar Yuanbaoshan ta birnin Chifeng dake jihar Mongoliya ta gida. Rubutun da wata karamar yarinya ta rubuta mata, sau da yawa yana haskawa a zuciyar ta, abin da ke cikin rubutun ya ba ta mamaki da kuma faranta mata rai sosai.

“Malama Sun, na gode da kika ba ni ilmi masu yawa game da kiyaye kai. A nan ina fada miki wani sirri, don Allah kar ki gaya wa wasu: na rasa mahaifiya ta, mahaifina ya fita waje domin aiki, kullum ina zama tare da kakana da kakata kawai. Sau da yawa, kawun makwabcin ya kan rungume ni da karfi, wanda hakan ya sa ba na ji dadi sosai. Kin ba mu darasi a kwanakin baya, inda na gane cewa, abun da ya yi min alama ce mai hadari. Kada ki damu, zan yi iyakacin kokarina na nisance shi nan gaba, idan ya ci gaba da yin haka, zan gaya wa manya, ko kuma in je neman taimako daga ‘yan sanda.”

Domin ayyukan da suka gudanar sun yi yawa, don haka, Sun Lan ba ta san wadda ta rubuta wannan ba. Ta ce, da ganin rubutun, ta yi matukar kaduwa, ba ta yi tsammanin akwai wata yarinya a kusa da ita da ta gamu da irin wannan abu ba. Abin farin ciki ne da gaske ayyukanmu sun inganta wayar da kan yara kan kare kansu. A ganinta, wannan shi ne nasarar da suka samu kan ayyukan da suke yi, kuma ta gano ma’anar ayyukansu.

A cikin wani aikin da rukuninsu ya yi, Sun Lan ta tambayi yara a aji na shida cewa, "Tun daga kuke kanana har zuwa yanzu, ko iyayenku suka taba gaya muku cewa ba a yarda a ga jikinku da kuma taba jikinku?" Amsar ba ta misaltuwa, kasa da kashi uku kadai na iyayen sun taba ambatar wannan batu!

Sun Lan ta fahimci cewa, yana da muhimmanci a wayar da kan iyaye game da kare yara, don haka a cikin laccocin da take yi wa iyayen dalibai, ta kan koya musu dama da dabarun ilmantar da 'ya'yansu kan batun jima'i. Mahaifin wata daliba ya gaya wa Sun Lan bayan kammala lacca cewa, “Malama Sun, a gaskiya ina so in tashi lokacin da na shigo kuma na ga wannan batun da za ki koya mana, ga ni namiji ne, bai dace ba na sauraro ilimin jima’i. Daga baya, na yi tunani, tun da na riga na zo nan, kawai na saurare shi. Amma, bayan kammala lacca, na samu ilmi kwarai da gaske, lallai ya taimake ni sosai, na gode sosai!"

Sun Lan ta ce bayan shekaru masu yawa, tun daga laccocin iyaye zuwa na kungiyoyin dalibai, har ma da tuntubar juna kan batutuwan da suka shafi daidaikun mutane, yayin da take kara jin kima da muhimmancin gudummawar da ta bayar, tana shirye ta ci gaba da zama ‘ya’yan ‘dandelion’ don kare yara yadda yakamata.

A hakika, Sun Lan ita ce misalan kungiyoyin zartarwa na "Dandelion" masu yawa. Idan aka kalli duk jihar Mongoliya ta gida, a dukkan birane 12 daga gabas zuwa yamma, ana iya ganin masu aikin agaji na "Dandelion" dake kokarin gudanar da ayyukansu.

A yankin ungalow dake kusa da makarantun na firamare da na sakandare da yawa a cikin garin Shanba na birnin Bayannur, akwai mata fiye da 60 da ke hayar gida a nan, domin raka ‘ya’yansu wajen karatu, baya ga yin wanki da girki da debo da sauke yara, galibin sauran lokutan ana kashe su ne da wasan mahjong, wasan kati, da yin hira da juna. Amma a gaskiya, yawancinsu iyalansu ba su da wadata. Aikin warware rikicin iyali na "Dandelion" ya ba su horo da jagoranci, tare kuma da taimaka musu wajen samun aikin yi bisa iyawarsu, hakan aka kara kudin shiga da suka samu, da kuma wadatar da rayuwarsu ta lokacin hutu.

Kamar aikin "Dandelion" da aka ambata a sama, a cikin 'yan shekarun nan, wasu kungiyoyin zaman al’umma masu yawa suna ta kokarin gudanar da ayyukan da ke cike da kauna.

Shou Lanlan, Daraktan Sashen Hakki da Bukatu na Kungiyar Mata ta Mongoliya ta gida, ta ce, tun daga shekarar 2017, sun zuba jarin musamman na RMB Yuan miliyan 7 a cikin kudade na musamman, don aiwatar da ayyuka guda 244 game da "Dandelion", kana sun daidaita rikicin aure da na iyali fiye da dubu 11, tare da gudanar da ayyuka iri daban daban sama da 3,600. Sun kuma yi aiki daidai da gidaje sama da 30,000 masu fama da matsaloli, masu cin gajiyar kai tsaye sun kai sama da dubu 450.