Waiwaye kan Hadin gwiwar Sin da Najeriya a shekarar 2022
2022-12-28 10:42:16 CMG Hausa
Tun lokacin da kasashen Sin da Najeriya suka kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu a ranar 10 ga watan Fabarairun shekarar 1971, dangantakar kasashen biyu take ta kara bunkasa, har ma suka fadada alakar zuwa fannoni daban-daban. Tun ma kafin kulla wannan alaka, jami'an kasashen biyu sun sha ziyartar kasashen juna a mabanbantan lokuta.
Najeriya ita ce, kasa mafi yawan al'umma da karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, yayin da kasar Sin ke zama babbar kasa mai tasowa mafi yawan al'umma, kana kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Yanzu haka, kasashen Sin da Najeriya na hadin gwiwa a fannonin aikin gona, da al'adu, ilimi, da kafofin watsa labarai, mata da matasa, harkokin cinikayya da ababan more rayuwa da sauransu.
A yayin da kasashen biyu ke raya alaka a tsakaninsu, sun kuma yi alkawarin kare manufofi da muradun juna da rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan juna da goyon bayan juna a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya da makamantansu. Matakan da suka haifar da da mai ido. Ci gaba na baya-baya nan shi ne, kammala kashi na farko na layin dogo a jihar Lagos dake Najeriya, wanda kamfanin kasar Sin ya gudanar, layin dogo mai amfani da lantarki na farko a yankin yammacin Afirka.
Haka kuma, sassan biyu sun lashi takwabin karfafa tuntubar juna don tabbatar da ganin an aiwatar da sakamakon da aka cimma, a yayin taron dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka (FOCAC) da shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)