logo

HAUSA

Sin ta fi mai da hankali kan hakikanin yanayin yaduwar cuta yayin kandagarkin annoba

2022-12-28 09:53:19 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata sanarwa a ranar 26 ga wannan wata, inda ta sauyawa cutar COVID-19 suna daga “novel coronavirus pneumonia” wato matakin cutar mai tsanani dake shafar huhu, zuwa “novel coronavirus infection”, kuma ta sanar da cewa, za ta sauya matakin yaki da cutar daga rukunin A zuwa rukunin B tun daga ranar 8 ga watan Janairun shekarar 2023 dake tafe, bisa dokar magancewa da jinyar cututtuka masu yaduwa ta jamhuriyar jama’ar kasar Sin. Ya zuwa wancan lokaci, ba za a kebe wadanda suka kamu da cutar ba, ba za a tantance wadanda suka yi mu’ammala da majinyata ba, kuma ba za a kebe yankunan hadari ba, kana ba za a dauki matakan yaki da cutar kan mutane da kayayyakin da suka shigo kasar daga ketare ba.

Matakin yaki da cutar da kasar Sin ta dauka ya kara inganta bisa tushen nazari da binciken da aka yi kan sauyawar kwayar cutar da hakikanin yanayin yaduwar cutar. Makasudin sauya matakin shi ne, ci gaba da nacewa kan manufar mayar da rayuka da moriyar jama’ar kasar a gaban komai.

Kwanan baya shahararren kamfanin hada-hadar kudi na kasa da kasa Morgan Stanley ya fitar da wani rahoto mai taken “Hasashe kan tattalin arzikin duniya bisa manyan tsare-tsare a shekarar 2023”, inda ake ganin cewa, karuwar tattalin arzikin duniya a shekara mai zuwa za ta gamu da matsala, amma tattalin arzikin nahiyar Asiya zai samu ci gaba yadda ya kamata, musamman ma a kasar Sin da kasar Indiya.

Ana iya cewa, ingantuwar matakan yaki da cutar a kasar Sin za ta kara kare lafiyar al’ummar Sinawa, haka kuma za ta ingiza farfadowar tattalin arzikin kasar. Ana sa ran ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. (Jamila)