Kasar Sin Tana Da Yakinin Samun Nasara A Yakin Da Take Yi Da Annobar COVID-19
2022-12-28 19:14:16 CMG HAUSA
A yayin da yake mayar da martani kan sharhin da majalisun ‘yan kasuwa na kasashen waje da dama da ke kasar Sin da ofisoshin diflomasiyya na wasu kasashe a kasar Sin, game da managartan matakan yaki da annobar cutar COVID-19 na kasar Sin, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labarai Larabar nan, cewa, kasar Sin tana da kwarin gwiwa cewa, yayin da take kula da lafiyar jama’a da rigakafin cututtuka masu tsanani, a hannu guda kuma, za ta hanzarta farfado da tattalin arziki da zamantakewar al'umma, tare da samun nasara wajen yaki da annobar.(Ibrahim)