logo

HAUSA

Kamfanin jiragen sama na Habasa zai dawo da jigila a Tigray dake hannun ’yan tawaye

2022-12-28 12:28:22 CMG Hausa

Kamfanin jiragen sama na Habasha wato Ethiopian Airlines, ya sanar da matakinsa na dawo da jigila a Mekele, babban birnin yankin Tigray dake hannun ’yan tawaye.

Shugaban kamfanin Mesfin Tasew, ya ce dawo da jigilar zai ba iyalai damar sake haduwa da saukaka farfado da ayyukan kasuwanci da inganta ayyukan bude ido da samar da dimbin damarmaki da al’umma za ta mora.

An tsara jigila zuwa Mekele a kullum, amma kamfanin ya ce zai kara yawan zirga-zirgar a kullum idan bukatar hakan ta taso.

Habasha wadda ita ce kasa ta biyu mafi yawan al’umma a Afrika, ta shafe shekaru 2 tana fama da rikici tsakanin dakarun gwamnati da mayakan kungiyar TPLF, lamarin da ya yi sandin mutuwar dubbai, inda miliyoyi kuma ke cikin matukar bukatar agaji. (Fa’iza Mustapha)