logo

HAUSA

’Yan sanda sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu satar mutane ne a Nijeria

2022-12-28 11:56:05 CMG Hausa

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu satar mutane ne yayin wani samame da ta yi a baya-bayan nan a jihar Delta dake kudancin kasar.

Kakakin ’yan sandan jihar Bright Edafe, ya shaidawa wani taron manema labarai a birnin Warri cewa, an kashe wadanda ake zargin ne a ranar Lahadi yayin da suke kokarin tserewa kame a birnin.

A cewarsa, wani ayarin jami’an sintiri ne ya kama wadanda ake zargin a ranar Asabar a Warri, bayan an gano kwanson harsasai 3 a cikin babur mai kafa 3 da mutanen suka yi amfani da shi. Yana mai cewa bayan tambayoyin da aka yi musu, an gano cewa suna cikin wata kungiyar mutane 5 dake satar mutane a yankin.

A ranar Lahadi ne kuma, wadanda ake zargin suka jagoranci ’yan sanda zuwa maboyarsu dake yankin, inda aka gano bindigogi biyu da adduna biyu.

Kakakin ya kara da cewa, a kan hanyarsu ta komawa ofishin ’yan sanda ne suka yi tsalle daga motar ’yan sanda domin tserewa, amma sai ’yan sanda suka yi musu mummunan raunin da ya kai ga mutuwarsu yayin da ake kai su asibiti. (Fa’iza Mustapha)